An kona ginin sakatariyar jam’iyar APC na jihar Imo


Wasu mutane da ake zargin batagari ne sun kona ginin ofishin sakatariyar jam’iyar ofishin na jihar Imo.

Wannan cigaban na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci wani zaman tattaunawa na bangarorin jam’iyar dake rikici, a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Taron ya tashi ba tare da cimma wata matsaya ba.

Rikici ya barke a jam’iyyar ta APC bayan da aka gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar a matakin matsabu.

Wani bangare na jam’iyar dake karkashin mataimakin gwamnan jihar,Eze Madumare, ya shirya zaben amma gwamnan jihar Rochas Okorocha ya nemi da a sake gudanar da wani sabon zaben.

A ranar Juma’a wasu da ake zargin batagari ne sun kunnawa ginin sakatariyar jam’iyar dake kan titin Okigwe a Owerri babban birnin jihar.

An rawaito cewa wutar ta lalata wasu takardu.

Shugaban jam’iyar na jihar, Hilary Eke, wanda ke biyayya ga Madumare ya ce ya sanar da yan sanda faruwar lamarin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like