An kona Wani Mutum Da Ake Zarginsa Da Aikata Fashi Da Makami A Jihar Anambra Wasu matasa da suka fusata sun kona wani mutum da ake zargin dan fashi da makami ne a Npor dake kusa da Onitsha a jihar Anambra biyo bayan fashi da akayi wa wani dan kasuwa akan titin Owerri zuwa Awka dake yankin. 

Wani sheda yafadawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa mutumin da aka yiwa fashin ya ciro kudi ne daga wani banki da misalin karfe uku na rana   kafin daga bisani mutumin da ake zargi da kuma wasu mutane biyu akan babur su kai masa hari.

A cewar majiyar wadanda ake zargi da aikata fashin sun kwacewa mutumin makudan kudade bayan da suka rinka binsa. 

” Nan danan mutumin ya ankarar da mutane abin da yake faruwa inda suka bisu suka samu nasarar kama mutum daya yayin da abokan fashin nasa suka tsere. 

“Basu bata lokaci ba suka kunnawa mutumin wuta kafin yan kungiyar sintiri dake yankin su isa wurin,” majiyar tace .

Duk kokarin da NAN sukayi najin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar yaci tura.

Da aka tambayi jami’in tsare-tsare na kungiyar yan sintiri dake yankin ya tabbatar da kona mutumin kana yace ana kokarin kamo wadanda suka tsere.

Amma kuma ya gargadi jama’a kan su guji daukar doka a hannunsu inda yakara da cewa su kyale jami’an tsaro suyi aikinsu. 

You may also like