An kone wani Dan OKADA  a lagos da Ransa. 


Dan OKADAn dai ya kasance daya daga cikin wadanda suke damun ‘yan unguwar Badagry da Fashi da makami,  inda suka qara yin fashi tare dashi da abokan aikin sa wanda suka canza kamanni a matsayin’ yan achaba.  
Sunyi fashin ne inda sukai shuka a idon makwarwa,  jami’an ‘yan sanda suka biyo su suna bude musu wuta,  sun samu nasar harbin tayar babur din daya daga cikin’ yan fashin,  nan suka zo suka kwace makamin hannun sa suka danka shi a hannun matasa.  

Matasa dai basi wata wata ba suka banka masa wuta dashi da babur din nasa,  ya kone kurmus. 

You may also like