An kori ma’aikata a jihar Yobe


A jihar Yobe a Nigeria wasu daga cikin ma’aikatan ƙananan hukumomi da aka sallama daga aiki sun koka cewa, an yi hakan ne ba bisa ƙa’ida ba.
Wani kwamitin tantance ma’aikata da gwamnatin jihar ta kafa ya sallami ma’aikata da dama a ƙananan huumomin Bade, Fika, Nangere, da Potiskum da kuma Nguru.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan da aka kora daga aiki Auwalu Mu’azu ya ce, shekarunsa 13 yana aiki, amma kuma an kore shi daga aiki.

Alhaji Mukhtari Adamu, shugaban wata ƙungiyar matasa a Potiskum, ya ce, yawancin waɗanda aka kora daga aiki matasa ne.Amma a martanin da ta mayar gwamnatin jihar Yoben ta bakin shugaban ma’aikatan jihar, Dauda Yahaya ta ce, an ɗau matakin sallamar ma’aikatan ne domin tabbatar da ma’aikatan gaskiya ne kadai ake biya albashi.

Dauda Yahaya ya kuma ce, binciken da suka yi ya gano cewa, wasu sun sanya matansu, da ‘ya’yansu cikin tsarin albashi ba tare da suna yin wani aiki ba.Jihar Yobe na cikin jihohin da suka fi fama da talauci a Nigeria.

You may also like