An kori Mugabe daga shugabancin Jam’iyyar ZANU-PF


Jam’iyar ZANU-PF mai mulkin ƙasar Zimbabwe ta kori shugaban ƙasar Robert Mugabe daga shugabancin jam’iyyar inda ta maye gurbinsa da tsohon mataimakinsa da ya kora, Emmerson Mnangagwa.

Korar Mnangagwa da mugabi yayi wanda akewa lakabi da “Kada” shine ya jawo sojojin kasar suka yi masa bore har ta kai ga juyin mulki.

Jam’iyar ta kuma kori maidakinsa Grace Mugabe, daga mukaminta na shugabar matan jam’iyar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters sun hadu ranar Lahadi inda suka cimma wannan matsaya.

Mugabe dan shekara 93 ya shafe shekaru 37 yana mulkin kasar tun bayan da ta samu mulkin kai daga kasar Birtaniya.

Mugabe ya dage cewa shine halattaccen shugaban kasar Zimbabwe.

A ranar Juma’a ne a karo na farko Mugabe ya fito bayyanar jama’a inda ya halacci taron yaye daliban wata makaranta dake birnin  Harare.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like