An kwantar da Dino Melaye a asibiti


An kwantar da sanata Dino Melaye a asibitin Zankili dake Mabuchi a babban birnin tarayya Abuja.

An kai shi asibitin ne sakamakon raunukan da ya samu lokacin da ya yi tsalle daga cikin motar yan sanda ya yin da take tsaka da tafiya a kokarin da yake na tserewa.

Motar daukar marasa lafiya ce ta kawo shi asibitin da misalin karfe biyar na yamma inda aka kwantar da shi.

Babu jami’an tsaro lokacin da ya isa asibitin.

Jaridar The Cable ta gano cewa yan sandan suna kan hanyarsu ta zuwa kotu da Melaye inda suka canza hanya suka bi wata daban.

Hakan ne yasa Melaye ya ga kamar ana kokarin tasa keyarsa ne ya zuwa jihar Kogi.

Melaye ya yi saurin dirga daga motar hakan yasa ya samu raunuka.

You may also like