An soki ministan al’adun India bayan ya ce gwamnati na bai wa ‘yan yawon bude ido shawarar kada su sa siketa kasar.
Mahesh Sharma ya ce “a jerin abubuwan da aka hana dakuma wadanda ba a hana ba ” wanda ake basu a filin jiragen sama na Indiya, yana basu shawarar kar su yi yawo su kadai da dare a kananan garuruwa.
Daga baya ya bayyana cewa yana magana ne “dangane da wuraren addini”, ya kuma kara da cewa ya yi maganane saboda ya damu.Ya sha yin bayanai na takalar fada, inda yake dora alhaki kan “kasashen yamma” na dabi’u marasa kyau a Indiya kuma a shekarar da ta gabata, ya ce fita yawon dare da mata ke yi, ba al’ada ba ce ta Indiya.
A ranar Lahadi ne dai yayi kalaman fusatarwa na baya-bayan nan, inda ya shaidawa manema labarai cewa ana bai wa ‘yan yawon bude ido “kayan maraba” a filin jiragen saman kasar.Cikin kayan har da katin da ke dauke da jerin abubuwan da ya kamata su yi da wanda bai kamata su yi ba.