Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sun mika kokon barar su ga mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar yayin zaben 2019. Shugaban Jam’iyyar Chief Ralph Nwosu ne yayi wannan kira yayin zantawa da jaridar Guardian.