An raba hular  yaƙin neman zaɓen Buhari a taron majalisar zartarwar tarayya


Yanzu haka dai za a iya cewa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ya fara kankama tun daga taron majalisar zartarwar tarayya na yau Laraba.

Adebayo shitu ministan sadarwa wanda shi ne shugaban kungiyar yaƙin neman zaɓen Buhari da Osinbajo a karo na biyu da ake kira Muhammadu Buhari/Osinbajo Support Group a turance.

Shitu wanda yazo da jaka cike da hulunan da aka rubuta ‘Continuity 2019: Muhammadu Buhari/Osinbajo’, ministan ya halarci zaman majalisar sanye da hular akansa kana ya rabawa wasu ministoci dake wurin.

Mintoci kaɗan kafin fara zaman majalisar Shitu ya miƙa jakar huluna ga sakatariyar majalisar.

 A makon da ya gabata ne ministan sadarwar ya jagoranci taron buɗe ofishin ƙungiyar a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

You may also like