An rabar da litar mai 14,400 kyauta a AbujaSashen Dake Lura da Albarkatun Mai, DPR a jiya ya rabar da litar  mai 14,400 kyauta ga masu ababen hawa a wani gidan mai dake kan hanyar Gwagwalada zuwa Deidei a Abuja.

An rabar da man kyauta ne saboda gidan man na sayar da shi fiye da farashin da aka kaiyade na ₦145 kan kowace lita kuma bashi da lasisin sayar da mai daga DPR.

DPR ya yin samamen wanda kwantirolan ta na shiyar Abuja, Abba Misau ya jagoranta sun kuma kama manajan gidan man.

Ya yin da yakewa manema labarai jawabi bayan samamen, Misau ya ce gidan man na aiki ne ba bisa ka’ida ba a yankin.

Ya ɗora alhakin sake bullar layuka a gidajen mai dake birnin tarayyar  kan rashin samar da mai akai-akai ga Abuja da kuma kewayenta.

“Amma mun samu tabbaci daga PPMC cewar za a cigaba da samar da man ba tare da yankewa ba,”yace.

 Mai gidan man, Danladi Eya yace ya sayi man ne daga wani dillalin mai dake da rijista.

You may also like