An rabawa masu ababen  hawa litar mai 2000 kyauta a Kaduna


Hoto:Daily Trust

Ofishin shiyar arewa maso yamma na DPR ya raba man fetur sama da lita 2000 kyauta ga wasu masu ababen hawa a Kaduna.

Ibrahim Chiroma, shugaban kwamitin kar ta kwana na haɗin gwiwa da sashen DPR ya samar ya fadawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa an gano man fetur din ne boye a gidan man SUL Nigeria Limited dake Rigachukun.

A cewar sa dillalin man yana sayarwa da yan bunburutu man idan dare yayi kuma an sha yi masa gargadi a lokuta da dama amma yaƙi ji.
Chiroma ya ce kwamitin kar ta kwana na haɗin gwiwa dake da mambobi daga dukkanin hukumomin tsaro ba shi da wani zaɓi face ya kwace man kana ya rabar da shi kyauta ga masu ababen hawa.
Yace kwamitin zai kwance kayunan bada mai dake gidan domin hakan ya zama darasi ga sauran masu aikata irin wannan dabi’a.

Ya kara jaddada cewa matakin da aka dauka wani bangare ne kawo karshen matsalar mai dake addabar ƙasarnan.

You may also like