An rage farashin lantarki a Ghana


160623140856_ghana_john_mahama_512x288_bbc_nocredit

Gwamnatin John Mahama a Ghana ta rage farashin wutar lantarki sakamakon tallafin Cedi miliyan 300 da ta bayar don saukakawa talakawan kasar nauyin biyan farashin wutar lantarkin.

A karkashin shirin tallafin a yanzu, masu anfani da wutar lantarkin musamman masu karamin karfi, zasu biya pesewa 34 a kan ko wani mizani na wutar lantarkin, maimakon pesewa 67 da suke biya a da.

Daga farkon wannan watan ne dai shirin ya fara.

Rage farashin ya biyo bayan korafin da al’ummar kasar ke yi cewa yana neman fin karfinsu da kuma alkawarin da shugaban kasar ya yi na cewa za a rage farashin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like