An Ragewa Dan Sanda Girma Bayan Samunsa Da  Laifin Cin Mutuncin Farar Hula A Jihar Kano 


Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta rage wa wani jami‘inta girma sakamakon cin zarafin ma‘aikacin banki. Rage mukamin dai ya biyo bayan cin zarafi da musgunawa wani ma‘aikacin banki da dansandan yayi ta hanyar sa shi yayi tsallen kwado da bashi wahala.

Kakakin rundunar, DSP Majiya, yace an rage wa dansandan girmane daga matakin Sajan zuwa Kofur, bayan anyi bincike an kuma same shi da laifi. Yace wannan hukuncin da rundunar tasu ta dauka zai zama darasi ga sauran masu amfani da kakinsu ko ikon su wajen musgunawa al‘umma ba gaira ba dalili.

Daga karshe ya ja hankalin ‘yan uwansa ‘yansanda da suyi aiki tsakani da Allah da yin adalci kamar yadda dokar aikin dansanda ta tanadar.

You may also like