
Asalin hoton, EPA
Humza Yousaf ya samu nasarar zama jagoran Jam’iyyar SNP a ranar Litinin bayan doke Kate Forbes
An rantsar da Humza Yousaf a matsayin shugaban yankin Scotland a wani ƙwarya-ƙwaryar buki a birnin Edinburgh.
Humza, ya zama musulmi na farko da ya riƙe wannan muƙami.
Majalisar dokokin Scotland ce ta zaɓe shi a matsayin shugaban yankin a wani zaman da ta yi ranar Talata.
Sabon jagoran Jam’iyyar ta SNP ya zama mutum na farko daga kabilar da ba ta da rinjaye da zai jagoranci gwamnati bayan samun yawancin kuri’un da aka kaɗa.
Shugabannin jam’iyyu na ɓangaren adawa guda uku – Conservative da Labour da kuma Libs – su suka kalubalance shi a zaɓen.
Zai fara kafa mukarraban gwamnatinsa a wannan mako, inda zai fuskanci shugabannin ƴan adawa a karon farko a taron amsa tambayoyi a ranar Alhamis.
Mr Yousaf ya samu nasarar zama jagoran Jam’iyyar SNP a ranar Litinin bayan samun kuri’u 26,032, inda ya doke Kate Forbes wadda ta samu kuri’a 23,890, sai kuma Ash Regan da ta zo na uku a zaɓen.
Mista Yousaf ya kasances sakataren lafiya na yankin Scotland kafin wannan zaɓe.
Duk da yadda yakin neman zaɓe ya zafafa, inda aka ga Ms Forbes na caccakar cancantar Mr Yousaf a wata muhawara a gidan talabijin, dukkan ƴan takarar da suka sha kaye sun taya sabon jagoran murna kan nasarar da ya samu, inda suka bukaci jam’iyyar da ta haɗa kai domin mara masa baya.
Da yake magana da gidan talabijin na ITV bayan nasarar da ya samu, ya kwatanta kansa da mutum mai sa’a, inda ya tabbatar wa jama’a cewa zai yi aiki tukuru wajen kawo wa yankin ci gaba.
Ya kuma ce zai jagoranci kamfe wajen ganin yankin ya samu ƴancin kai.
Ya ƙara da cewa “al’ummar Scotland na son ƴancin kai a yanzu, kuma za mu kasance waɗanda za su jagoranci tabbatar da ganin hakan ya samu.”
Mr Yousaf ya kuma ce zai tambayi gwamnatin Birtaniya da ta bayar da damar sake gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a nan take a ƙasar.
Fadar Downing Street tuni ta ce ba za ta canza matsayar ta kan adawa da kuri’ar jin ra’ayin ba, inda mai magana da yawun firaministan ƙasar ya ce zai fi mayar da hankali kan batutuwan da suke da muhimmanci ga jama’a kamar rage hauhawar farashin kayayyaki da kuma magance tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Wane ne Humza Yousaf?
Asalin hoton, PA Media
Mr Yousaf tare da iyayensa Shaaista da Muzaffar
Mahaifinsa ɗan asalin ƙasar Pakistan ne, inda ya koma Scotland da iyalansa a shekarun 1960. An haifi mahaifiyarsa a ƙasar Kenya.
Mista Yousaf ya sha yin magana kan batun wariyar launin fata da ya fuskanta.
Mista Yousaf ya halarci makarantar Hutcheson da ke birnin Glasgow.
Daga nan ya wuce zuwa Jami’ar birnin Glasgow, inda ya karanci fannin siyasa.
Ya yi aiki na ƙanƙanin lokaci a wani wurin buga waya kafin ya fara zama mataimaiki ga ɗan majalisar jam’iyyar SNP Bashir Ahmad da kuma Alex Salmond a majalisar dokokin Scotland.
An zaɓi mista Yousaf a matsayin ɗan majalisar yankin Glasgow a 2011, inda daga baya mista Salmond ya ɗaga likafarsa zuwa ministan Turai da ci gaban ƙasashen waje.
Ya zama ministan sufuri a 2016 wanda ya ba shi damar zama mutum na farko daga kabilar da ba ta da rinjaye da ya samu nasarar shiga majalisar dokokin Scotland.