An rantsar da shugaban Brazil Lula ga wa’adin mulki na ukuLula da Silva

Asalin hoton, Getty Images

Sabon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, mai ra’ayin kawo sauyi, ya sanar da dubban magoya bayansa da suka hallarci bikin rantsar da shi a Brasilia babban birnin kasar, cewa babban aikin da ke gabansa shi ne na hada kan ‘yan kasar.Shugaban ya ce wagegen gibin da ke tsakanin attajiran kasar da matalauta ya zama karfen-kafa ga tsarin dimokradiyya, sannan ya lashi takobin yin mulki domin kowa ne dan kasar ya amfana.Bayan da aka kammala bikin rantsar da shi, Shugaba Lula ya shaida wa majalisar kasar Brazil cewa zai sake gina kasar daga matakin da ya kira na matsanancin lalacewa, musamman ma dajin nan na Amazon – duka karkashin matsalolin da ya gada daga Jair Bolsonaro.Shugaba Lula ke nan ke cewa “Alhakin kulawa da dajin amazon da ma wuraren da dumbin albarkatun karkashin kasa suke kamar karfe da man fetur da tarin ruwan ruwan dadi da ke bulbulowa daga karkashin kasa da kuma hanyoyin samar da hasken lantarki wadanda ba sa gurbata muhalli.”Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like