An Raunata Jagororin Kwankwaso A Hawan Daushe Da Sarki Keyi Shekara Shekara A Jihar Kano Da dukkan alamu wutar rikici tsakanin Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Dan Jarida Nasiru Salisu Zango ya ruwaito cewa, an raunata manyan makusantan Kwankwaso da suka hada da tsohon sakataren gwamnatin Kano Engr Rabiu Suleman Bichi, tsohon kwamishinan kasa da tsare tsare Yusif Bello Danbatta da Yahya Musa Kwankwaso wanda shaqiqin tsohon gwamnan Kano ne Sanata Rabiu Kwankwaso da sauran mutane da dama. A lokacin da muka kai ziyara asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano mun iske an tafi da Engr Rabiu Suleiman Bichi dakin hoto bisa raunin da aka yi masa a ka.

Wasu da aka jiwa raunin sun zargi dan majalisar jiha mai wakiltar Birni da Kewaye Baffa Babba Dan Agundi da rafkawa tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano kuma babban yaron Kwankwaso kokara. Jaridar SARAUNIYA  ta yi ta kokarin tuntubar Baffa Babba Dan Agundi domin jin ta bakinsa, amma hakan mu bai kai ga cimma ruwa ba. 

Sai dai duk da haka za mu ci gaba da bibiya.

You may also like