An rufe gidajen mai 8 a Kano 


Hoto: Channels Tv

Sashen dake kula da albarkatun mai, DPR na kamfanin NNPC, ya ziyarci gidajen mai 166 a jihar Kano inda ya rufe guda 8 daga ciki waɗanda aka samu da boye man da kuma sayar da shi akan farashi fiye da ka’ida.

Yayin duba gidajen man, mukaddashin kwantirola me kula da aiyuka a ofishin hukumar dake Kano, Paul Jhezi ya ce an gudanar da ziyarar gani da ido zuwa gidajen mai  a dukkanin kananan hukumomi 44 dake jihar.

Jhezi ya ce makusudin ziyarar zuwa gidajen man shine don tabbatar da cewa an kawar da layukan mai a jihar idan aka yi duba da ƙarin yawan mai da jihar ta samu daga kamfanin NNPC.

Yace tuni aka kara tura karin jami’ai zuwa sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da cewa gidajen mai sun bi ka’ida wajen sayar da mai.

You may also like