An rufe kofar da ya kamata Leeds ta dauki Iraola – BalagueAndoni Iraola

Asalin hoton, Getty Images

Rayo Vallecano ta rufe duk wata kafa da ya kamata Leeds ta dauki kociyanta, Andoni Iraola, in ji dan Sifaniya, Guillem Balague masanin kwallon kafa.

Iraola, mai shekara 40, ya kai kungiyar da ke Madrid mataki na biyar a teburin La Liga, bayan wasa 20 a bana da tazarar maki uku da gurbin ‘yan Champions League.

Ya ja ragamar kungiyar da ta ci Barcelona a bara, ya kuma doke Real Madrid 3-2 a cikin watan Nuwamba.

Iraola na son ya tattauna da Leeds United, don maye gurbin Jesse Marsch, wanda ta kora ranar Litinin, amma Vallecano ba ta bashi izini ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like