An rufe matatar mai dake Kaduna saboda rashin ɗanyen man fetur


Matatar man fetur dake garin Kaduna wacce ake kira Kaduna Refining and Petrochemical Company (KRPC) a turance  ta dakatar da aiyukanta saboda rashin ɗanyen mai da za ta tace.

Abdullah Idris, daraktan dake kula da aiyuka shine ya shedawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN haka a Kaduna.

Yace matatar da aka ƙaddamar da ita a shekarar 1980 tana aiki ne kaso 60 cikin ɗari “amma an dakatar da aiki a ranar 15 ga watan Janairu saboda rashin ɗanyen man fetur.”

A cewarsa kafin a dakatar da aiki, matatar na samar da litar mai miliyan huɗu a kowace rana.

Idris ya ƙara da cewa matar na kuma samar da man disel lita miliyan 2.5 da kuma man kananzir lita miliyan 1.6 a kowacce rana.

You may also like