An Rushe Batun Karawa Shugabannin APC Wa’adi


Kafatanin gwamnonin jam’iyyar APC guda 24 sun amince da kudirin Shugaban kasa Muhammad Buhari na a mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar gurin zabar sababbin shuwagabannin jam’iyyar.

Gwamnan Jahar Zamfara, Alhaji Abdulaiziz Yari ne ya bayyana hakan ga manema labaran fadar shugaban kasa a yau bayan Buharin ya gana da wasu gwamnoni.

A satin da ya gabata, yayin taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin tsawaita wa’adin mulkin John Odigie-Oyegun na shugabancin jam’iyyar a matsayin saba doka.

“Mun nemi shawarar dukkan gwamnonin APC guda 24, sannan mun gane dukkansu suna kan layin da shugaban kasa ya bi na zamu mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu, kuma zamu mutuntu kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijeriya. Saboda haka, gaba dayanmu mun amince da zamu gabatar da taruka a dukkan matakai – karamar hukuma, jaha, da kasa baki daya.” Gwamna Yari ya fada.

You may also like