Wani abin tashin hankali da ya auku a garin Birnin Gwari jihar Kaduna a daren Asabar shine yadda aka sace amarya sukutum da kawayen ta su goma a daidai lokacin da za a kai ta dakin mijinta.
Wannan al’amari ya tada wa mutanen garin Birnin Gwari hankali matuka.
Wani tsohon shugaban karamar hukumar Birnin Gwari, da baya so a fadi sunan sa, ya tabbatar wa wakilinmu wannan abin tashin hankali da ya faru a garin.
Ya ce maharan sun tare motar dake dauke da amarya ne da kawayenta da kamar karfe 8 na dare, sannan su ka yi awon gaba da su cikin kungurmin daji.
“Yanzu dai abin ya zama ruwan dare a Birnin Gwari, kusan kullum sai kaji irin wannan tashin hankali. Muna rokon gwamnati ta taimaka wajen shawo kan wannan matsala”.