An Sace Basarake A Jihar Kogi
Wasu mahara sun sace Sarkin Aghara a karamar hukumar Kabba-Bunu da ke jihar Kogi a tsakiyar arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust da ta ruwaito labarin ta ce an kashe wata mata a fadar Sarki Pa David Obadofin yayin harin da ‘yan bindigar suka kai da sanyin safiyar Talata.

Baya ga Pa Obadofin da suka sace, ‘yan bindigar har ila yau sun yi garkuwa da wasu manyan fadawa biyu.

Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun fada farfajiyar fadar ne suna harbin kan mai uwa da wabi a lokacin da suka kai harin.

Rundunar ‘yan sanda jihar ta Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin tana mai cewa ta tura jami’anta don kubutar da mutanen tare da kama ‘yan bindigar.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like