An Sace Mahaifiyar Mai Gidajen Man Shema Petroleum A Katsina


An sace tsohuwar mai shekaru 82 a duniya a gidanta dake Bayan Area, a cikin garin Dutsin-Ma .

Wani ganau ya shiadawa majiyarmu cewa ‘yan bindigar sun je gidan tsohuwar ne wajen su biyar bisa babura da wajen misalin 1:30ny na jiya Jumma’a, inda suka yi harbe harbe sannan suka afka cikin gidan suka dakko matar.

A lokacin artabu da barayin sun raunata mijinta Alhaji Abdullahi, sannan suka harbi makwabcinsu Usman Barkiya har sau biyu a kokarinsa na ganin ya ceci tsohuwar.
.

“A lokacin da mashin dinsu daya ya lalace a kofar gidan Barkiya, ya yi yunkurin ceton Hajiya, amma suka harbe shi sau biyu a hannu da cikinsa , yanzun haka yana babban asibiti ana duba lafiyarsa”, kamar yadda ganau din ya shaida.

.
Mun samu labarin cewa dan nata mai kamfanin gidajen man Shema Petroleum a duk fadin kasar nan Nagogo Mammam Nagarhi, ya ziyarci mahaifiyar tasa kwana daya kafin afkuwar lamarin.

.
A lokacin da jaridar Daily Trust ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni suka dukufa wajen fafutukar ceto ta.

You may also like