An Sace Wani Oba A Lagos, Ana Garkuwa Da Shi


 

Iyalan Oba Goriola Oseni, Oniba na kasar Ibaland dake Jihar Lagos, amma ‘yan sanda sun ce su na kokarin kwato shi.

‘Yan sanda a Jihar Lagos, kudu maso yammacin Najeriya, su na farautar wasu ‘yan bindiga da suka sace wani basarake mai suna Oba Goriola Oseni, wanda shine Oniba na kasar Ibaland.

Rahotanni sun ce an sace wannan basaraken ne tare da wani dan kasuwa da wata mace da kuma danta mai watanni 3 da haihuwa a masarautarsa dake Ikorodu, kusa da bakin gabar ruwan Lagos, dab da iyaka da Jihar Ogun.

Wannan yankin da aka sace basaraken, yayi kaurin suna wajen ‘yan bindigar da suka saba fasa bututun mai su na satarsa. Amma a yanzu da yake an kara karfafa tsaron bututun, ana fuskantar karuwar sace mutane domin neman kudin fansa a wannan yanki.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Lagos, Mr. fatai Owoseni, ya ki yarda ya tattauna wannan batu a lokacin da wakilinmu ya tuntube shi.

Sai dai kuma sabon mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda mai kula da jihohin da wannan abin ya faru, Abdulmajid Ali, wanda shine tsohon kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Ogun, yace a yanzu ana yin sintirin hadin guiwa a tsakanin ‘yan sanda da sojojin ruwa har ma da na kasa a wannan yanki, domin shawo kan irin wadannan ‘yan bindigar.

Wani dan’uwan wannan basarake da aka sace, ya fadawa ‘yan jarida cewa har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntubi niyalansa ba.

Su kuwa ‘yan’uwan dan kasuwar da aka sace tare da basaraken, sun ce ‘yan bindigar sun tuntube su a kan su biya fansar naira miliyan 30 domin a sako shi. Suka ce sun yi tayin zasu biya naira miliyan 3, amma har yanzu ba su ji daga bakin ‘yan fashin ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like