An Sace Wasu Manoma A Jihar Zamfara 


Rahotannin dake fitowa daga Dajin Dansadau a jihar Zamfara sun nuna cewa a safiyar jiya Lahadi wasu mutane da ba’a san ko su wanene ba da ake sa ran barayin shanu ne, sun sace wasu manoma dake noma a cikin dajin Dansadau.
Daga cikin wadanda aka zargin an sace akwai wani babban ma’aikacin gwamnati a ma’aikatar kudi ta jihar Zamfara mai suna Surajo Bello Buzu Kaura, wanda wata majiya daga iyalan wanan ma’aikaci ta bayyana cewa suns amu labarin sace dan uwansu tare da wasu manoma uku a lokacin da suke aikin feshin maganin kwari a gonarsa dake yankin. Wanda yanzu haka motarsa kadai ce aka isko a gonar.
Rahotanni na nuna cewa tuni aka sanar da jamian tsaro wanda ake sa ran za su dauki mataki duk da yake ba a ji tabakinsu ba.

You may also like