
Asalin hoton, OTHER
A Ingila jaridar Guardian ta rawaito cewa ana neman fam miliyan 500 ga mai son sayen kungiyar kwallon kafa ta Everton da ke birnin Liverpool.
Kungiyar ta Merseyside na zaune ne a matsayin ta 19 a teburin Premier League da maki 15 a cikin wasanni 20, kuma dama dangantaka ta yi tsami tsakanin masu kungiyar da magoya bayanta, da ke son kungiyar ta fita hannunsu.
Yanzu haka Everton na neman kocin da zai ceto ta daga fadawa ukun karshe, bayan da ta sallami tsohon dan wasan Ingila da Chelsea Frank Lampard, wanda ya kasa cin wasa a gasar tun watan Oktoban bara.
Sai dai kuma jaridar Liverpool Echo ta ce mai kungiyar Farhad Moshiri, ya yi watsi da labaran da ke yawo cewa za a sayar da Everton, inda ya kafe cewa ya shirya ci gaba da rike kungiyar.
Anan kuma da yiwuwar Arsenal ta yi takara da Chelsea kan dan wasan tsakiyar Brighton, Moises Caicedo, a cewar Evening Standard.
To amma Times ta rawaito cewa Seagulls sun saka farashin fam miliyan 100 ga dan kasar Ecuador din.
Sai Independent, da ta rawaito cewa Everton na ci gaba da tattaunawa da Marcelo Bielsa don ya zama kocin kungiyar, duk da tana duba yiwuwar nada tsohon kocinta Sam Allardyce.
Sai dai Bielsa ya ce babu tabbas yana son karbar aikin. Akwai kuma kocin West Brom Carlos Corberana a jerin wadanda Everton ke nema, in ji jaridar Times.
Asalin hoton, OTHER
Telegraph ta rawaito cewa Leicester City na harin dan wasan gefen Leeds Jack Harrison.
Dan wasan Senegal da Villareal Nicolas Jackson, zai yi gwajin lafiya a Bournemouth ranar Laraba, yayin da kungiyoyin biyu ke shirin kulla cinikin fam miliyan 20, in ji Guardian.
Cherries din na kuma tattaunawa da Roma don duba yiwuwar sayen mai tsaron bayanta, Vina. (90 min)
Nottingham Forest na son sayen golan Costa Rica Keylor Navas daga PSG, in ji jaridar Mail.
Chelsea ta bude tattaunawar tsawaita zaman mai tsaron bayanta Thiago Silva, yayin da kwantiraginsa ke shirin karewa a karshen kaka. (Athletic)
Ana tattaunawa tsakanin Leeds United da Juventus kan kulla cinikin dan wasan Amurka, MacKennie, a cewar Fabrizio Romano.
Wata majiya ta ce Arsenal ma ta yi bincike kan MacKennie. (Gazzetto dello Sport)
Kazalika Gunners ne kan gaba wurin son sayen mai tsaron bayan Real Valladolid, Ivan Fresneda. (Football Insider)