An sake buɗe filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja bayan da aka rufe filin na wasu ƴan sa’o’i bayan da wani jirgin sama ya samu hatsari.
Hanyar tashi da saukar jiragen sama dake filin an rufe ta bayan da wani jirgi mallakin kamfanin Nest Oil ya kauce daga hanyar ta shi da saukar jiragen lokacin da yake ƙoƙarin sauka.
Har zuwa ƙarfe 6:35 na yamma jirage ne kawai suke sauka ba tare da wasu sun tashi ba.
Hadi Sirika ministan harkokin sufurin jiragen sama ya bada sanarwar cewa za’a rufe filin jirgin na tsawon mintuna 30 domin hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasa FAAN ta ɗauki matakan kariya.
Wani sheda da ya ganewa idonsa abin da yafaru ya fadawa jaridar The Cable cewa sai da jami’an hukumar ta FAAN suka yi amfani da hannu wajen kawar da jirgin daga kan hanyar tashi da saukar jiragen.