An Sake Bude Sansanin MasubYiwa Kasa Hidima A YolaAn sake bude sansanin masu yi wa kasa hidima na garin Yola fadar jihar Adamawa bayan rufe shi tsawon shekaru uku da suka gabata sakamakon rikicin Boko Haram. 
Bude sansanin ya zo ne biyo bayan nasarar da sojojin Nijeriya ke samu a kokarin murkushe auyukan ta’adanci.
Sakataren dake horas da masu yi wa kasa hidima a jihar, Malam Muhammed Abubakar ya ce suna sa ran cewa masu yi wa kasa hidima dubu biyu da dari biyar ne za su iso jihar domin aikin yi wa kasa hidima.

You may also like