An Sake Daga Shari’ar Bafarawa Zuwa Watan Maris



A zaman da Kotu na jiya da ake yi wa tsohon gwmnan jihar Sakkwato, Alh Attahiru Dalhatu Bafarawa an dage shari’ar sai 17 ga watan Maris.
Zaman kotu mai shari’a Bello Abbas ta dage sauraren shari’ar da ake yi a tsakanin Bafarawa da gwamnatin jihar Sakkwato.  
Shari’ar wadda ta shafe shekaru fiye da goma sha daya ana ci gaba da kawo shaidanni tare da sauraren hujjoji daban-daban.
Wadanda ake karar da suka kunshi tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da tsohon Sakataren gwamnatin jihar Muhammadu Maigari Dingyadi,da wasu jami’an gwamnati da ‘yan siyasa ne suka halarci zaman Kotun na jiya.

You may also like