An Sake Kai Harin Kunar Bakin Wake A Jami’ar Maiduguri Kusan sa’o’i 48 kenan bayan da wasu yan kunar bakin wake suka kai hari a jami’ar Maiduguri,sai gashi a yau da safe  wani dan kunar bakin wake ya tayar da bom din da yake dauke dashi, a jikin katangar da ta kewaye jami’ar. 

kwamishinan yansandan jihar Borno, Damian Chukwu, yace harin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe. 

Yace dan kunar bakin waken ya buya ne kusa da makarantar sakandire ta jami’ar, inda ya tayar da bom din da yake jikinshi bayan da ya hango jami’an tsaro sun nufo inda yaake. 

Yace babu wani da ya jikkata sakamakon kai harin. 

Wannan harin dai shine na uku cikin kasa da mako biyu kuma ya kara jefa shakku da fargaba a zukatan malamai da kuma daliban jami’ar. 

Jami’ar dai na wajen birnin Maiduguri kan hanyar zuwa Bama. 

Bayan katangar jan bulo dake gaban jami’ar babu wani shinge a bayan jami’ar ,ana ganin haka shi yabawa yan ta’adda damar shiga jami’ar cikin sauki. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like