An Sake Kama Alkalai Biyu A Kaduna


A yayin da ake ci gaba da cece ku ce kan kama wasu manyan AlkalaI bakwai, rundunar tsaro na farin kaya( DSS) sun sake kama wasu Alkalai biyu a jiya Laraba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Alkalan biyu da aka kama sun hada da Mai Shari’a Bashri Sukola da Ladan Manir wadanda ke Babban kotun jihar Kaduna.
A yau ne kuma ake sa ran hukumar da ke kula da kotuna ta kasa(NJC) za ta bayyana matsayinta game da matakin kama alkalan bayan kwanaki uku da hukumar ta kwashe tana taron gaggawa.

You may also like