An Sake Kashe Wani Dan Najeriya A Kasar Afrika ta Kudu


An harbe wani dan Najeriya har lahira mai suna,Jelili Omoyele, dan shekara 35 dake gyaran wayar salula a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afrika ta Kudu ce ta bayyana haka.

Shugaban kungiyar Adetola Olubajo ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, haka ta wayar tarho daga birnin Johannesburg cewa Mista Omoyele wanda akafi sani da suna,Ja Rule,dan asalin garin Ibadan ta jihar Oyo an harbe shi ne a wani wurin ajiye motoci dake lardin Gauteng.

A wata tawagar bincike da ta ziyarci wurin da abun ya faru  karkashin jagorancin sa da kuma jami’in dake kula da walwala na kungiyar sun gana da wani sheda,Sipususo Mkalipi, matukin motar taso dan kasar ta Afirka ta Kudu wanda ya tabbatar da kisan.

“Marigayin da dan wanda yake Kula da wurin ajiye motocin sun samu sabani kan kudin haya R300 kwatankwacin ₦11,400.

“Shedar ya ce  marigayin ya yanke shawarar barin motarsa har zuwa ranar Litinin saboda bashi da kudin biya amma kuma, yaron mai kula da wurin ya harbeshi lokacin da ya juya ya nufi hanyar fita daga wurin.

“Omoyele ya rasu yan mintoci kadan bayan harbin da akayi masa,” yace.

 Mista Olubajo yace Mista Mkalipi shine direban tasi din da ya kawo Omoyele wurin ajiye motocin.

Tuni dai aka mika batun hannun yan sanda.

You may also like