An sake yin garkuwa da mutane fiye da 25 a Birnin Gwari


Hoto:Daily Trust

Sama da mutane 25 aka yi garkuwa da su akan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua dake jihar Kaduna a ranar Alhamis.

Wasu majiyoyi sun nuna cewa masu garkuwa da mutanen sun bulla ne a wani wuri dake tsakanin ƙauyukan Kiryoyi da kuma Maganda dake karamar hukumar Birnin Gwari.

An rawaito cewa sun tsayar da motoci inda suka tasa keyar fasinjojin dake ciki ya zuwa cikin daji.

Shugaban kungiyar NURTW a karamar hukumar Birnin Gwari, Alhaji Danladi Idon Duniya ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da aka yi da shi ta wayar tarho.

“Bani ya kamata na fada maka yawan mutanen da aka sace ba, amma suna da yawa watakila 25 ko kuma sama da haka.Bazan iya fada ba, amma dukkanin fasinjojin dake cikin motocin anyi garkuwa da su,” ya ce.

“Sun tsayar da motoci biyar daya daga cikin direbobin dake tuka mota kirar Golf ya samu nasarar tserewa.wannan ne halin da muke samun kan mu a ciki akan hanyar, muna kira ga hukumomi da su taimaka mana wajen shawo wannan matsalar.

“Mutane baza su iya zuwa gona ba baza kuma su iya yin tafiye-tafiye ba, lamarin ya yi muni sosai.”

Yin kurin samun, Aliyu Mukhtar mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, ta wayar tarho ya ci tura.

You may also like