An Saki Mutane 1,250 Da Aka Wanke Daga Zargin Alaka Da BokoHaram 



Rundunar Sojan Nijeriya ta saki mutum 1,250 wadanda tun farko aka tsare su bisa zargi suna cikin kungiyar Boko. Haram.
Kwamandan barikin Maimalari da ke Maiduguri,  Birgediya Janar Victor Ezugwu ya ce an saki mutanen ne bayan umarnin da Janar Burutai ya bayar kan cewa a saki duk wanda aka tabbatar ba ya da alaka da kungiyar wanda a cewarsa ana Sakin mutanen ne tsarin rukuni rukuni.
Ya kara da cewa nan wata mai zuwa za a sake Sakin wasu mutanen. Ya ce rundunar na iyakacin kokarinta wajen samar da yanayin zama da na abinci mai kyau ga wadanda ake tsare da su

You may also like