An saki wani mutum bayan kuskuren ɗaure shi tsawon shekara 28Lamar Johnson
Bayanan hoto,

Lamar Johnson

An saki wani ɗan ƙasar Amurka wanda aka yi kuskuren ɗaurewa a gidan yari na tsawon shekara 28 a Missouri bayan zargin sa da laifin kisa, duk da ya sha musantawa.

A ranar Talata ne wani alkali David Mason a kotun St Louis, ya yanke hukuncin da ya wanke mutumin mai suna Lamar Johnson, mai shekara 50.

Alkalin ya ce ya yanke hukuncin ne bayan wasu shaidu biyu sun gabatar da gamsassun hujjoji da ya yadda da su da kuma suka nuna cewa mista Johnson ba shi da laifi.

An yanke masa hukunci ne bayan da aka zarge shi da laifin kashe wani mai suna Marcus Boyd a shekarar 1994.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like