An sako dan gidan Atiku bayan an tsare shi na dan wani lokaci


Wata kotun majistire dake zamanta a yankin Tinubu a jihar Lagos ta bada umarnin a saki, Aminu dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Tun farko alkalin kotun ya bada umarnin a tsare Aminu kan saba umarnin kotun.

A ranar 11  ga watan Oktoba ta nemi Aminu da ya gabatar da yaron har zuwa lokacin da zata yanke hukunci kan shari’ar .

Lokacin da ake gabatar da shari’ar a ranar Laraba, lauyan Aminu ya sanar da kotun cewa mutanen biyu sun amince su santa kansu awajen kotu.

Amma Ethel Okoh, lauyan tsohuwar matar Aminu yace bashi da masaniyar shirin sasantawa a wajen kotun.

Bayan haka ne alkalin kotun ya yi umarni a tsare Aminu har sai ya kawo dansa dan shekara 8 da ake zargin ya raba shi da mahaifiyarsa, Fatima Bolori.

Kotun daga bisani ta bada umarnin a sake shi bayan da aka kawo yaron inda ta damka shi a hannun mahaifiyarsa har zuwa nan da kwanaki 10.

Auren Fatimo da Aminu ya mutu a shekarar 2011 bayan sun haifi yaya biyu.

You may also like