An sako shugaban gidan ajiye namun daji na Ogba da aka sace 


Bayan ya shafe sama da makonni uku a hannun masu garkuwa da mutane, Andy Ehanire, shugaban gidan ajiye namun daji na Ogba dake Benin babban birnin jihar Edo, masu garkuwa dashi sun sake shi.
An ce an sake shi a wani wuri da ba a bayyana ba dake garin Warri  mai dinbin arzikin mai na jihar Delta.

Har yanzu dai babu cikakken bayani kan yadda Ehanire ya samu yan cin sa.

Tuni dai ya hadu da iyalinsa dake Benin babban birnin jihar.

Sakin nasa na zuwa ne bayan bincike mai tsanani da yan sanda suke tun bayan da aka sace shi a cikin watan Satumba, lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari gidan ajiye namun dajin inda suka kashe yan sanda uku dake aikin samar da tsaro a wurin.

Mai magana da yawun rundunar yandan jihar, DSP Moses Nkombe, wanda ya tabbatar da sako Ehanire yace an cimma wannan nasara ne saboda jajircewar rundunar yan sandan jihar.

 An samu tsaiko ne wajen ceto Ehanire ne , saboda yadda wadanda suka yi garkuwa da shi suka rika canza wurare.

You may also like