An sako shugaban jam’iyyar PDP na jihar Plateau da sauran mutane 4 da akayi garkuwa da su


Shugaban jam’iyar PDP na jihar Plateau, Damishi Sango da kuma sauran mutane huɗu da akayi garkuwa da su ranar Laraba sun shaki iskar yanci.

Sango,da yan tawagarsa an sace su ne a wajejen Jere dake jihar Kaduna lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja domin halartar babban taron jam’iyyar PDP da akayi ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

Sakataren yada labaran jam’iyar PDP a jihar yace tun farko masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su miliyan ₦100 amma daga baya suka amince za su karbi miliyan ₦40.

Wani mutum daga iyalan tsohon ministan ya shedawa wakilin jaridar Daily Trust cewa tsohon ministan ministan wasannin sun samu yancin su ne da yammacin jiya kuma yanzu haka suna Abuja.sai dai bai iya tabbatarwa ko anbiya miliyan ₦40 din da aka nema ba.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Plateau, ASP Tyopev Terna ya tabbatar da sako mutanen.

You may also like