An samu karancin fitowar mutane a tashoshin zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar yau a jihar Kano.
Wannan dai ba baƙon abu bane idan aka yi duba da yadda zaɓen ƙananan hukumomi ke gudana a jihohin ƙasarnan.
Hakan baya rasa nasaba da yadda mutane suke ganin cewa zaɓen tamkar naɗi ne domin a koda yaushe ƴan takarar jam’iya mai mai mulkin jihar sune ke nasara a zaɓen.
A wasu tashoshin zaɓe ma’aikatan zaɓen basu samu halartar wurin ba har zuwa lokacin da aka rufe kada kuri’a.ya yin da wasu tashoshin aka samu isar kayayyakin zaɓen a makare.
Har ila yau a wasu tashoshin zaɓen an samu ƙananan yara a layukan kaɗa kuri’a da shekarunsu basu kai yin zaɓe ba.