
Asalin hoton, Getty Images
Masana a ɓangaren tsaro sun buƙaci hukumomi a Najeriya su ƙarfafa haɗin kai tsakanin gwamnatoci don inganta yaƙi da ayyukan ƴan bindiga masu addabar ƙasar.
Sun kuma buƙaci mahukunta su inganta tsarin tafiyar da lamurran tsaro ta yadda ba za a samu giɓin da zai ta’azzara matsalar ba.
Waɗannan shawarwarin na cikin rahoton da wani kamfanin tsaro mai suna Beacon Consulting ya fitar inda ya ƙiyasta cewa an samu ƙaruwar kashe-kashen mutane sanadin hare-haren da ƴan bindiga ke kai wa a sassan ƙasar cikin watan Nuwamban da ya wuce.
“An samu ƙari na yawan mace-mace da suka zarce kashi 50% daga watan Oktoba zuwa Nuwamban bana”.
Dr Kabiru Adamu shi ne shugaban kamfanin kuma a cewarsa, talauci na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ta’azzara matsalar tsaro a ƙasar.
Ya ba da misali da wani rahoto da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar game da ƙiyasin mutanen da ke fama da talauci da ya kai miliyan 330 inda ya ce galibi ƴan bindigar na amfani da talauci wajen cimma burinsu.
Dr Kabiru Adamu ya ƙara da cewa duk da ƙokarin da gwamnati take iƙirarin yi wajen dakile hare-hare a ƙasar, har yanzu ƴan bindiga na bin waɗansu hanyoyi suna samun kuɗi.
Ya ce “wani rahoto daga ɓangaren da ke sa ido kan yadda ake tallafawa ko ɗaukar nauyin ta’addanci, rahoton ya nuna cewa akwai wani giɓi da ƴan ta’adda ke amfani da shi wajen samun kuɗaɗe.”