Gwamna Oluwarotimi Akeredelu na jihar Ondo ya tabbatar da ɓarkewar cutar Lassa a Jihar, yace gwajin da akayi a dakin gwaje-gwajen kimiya ya tabbatar da mutane 36 dake ɗauke da cutar da suka haɗa da 9 waɗanda suka mutu.
Akeredelu wanda ya bayyana haka a Akure cikin wani jawabi na kai tsaye da aka watsa ta kafafen yaɗa labarai dake jihar a daren ranar Asabar, yace mutane 108 ake zargin sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa a ƙananan hukumomi 8 dake jihar.
“79 daga cikin wadanda ake zargin sunkamu da cutar bayan gwajin da akayi, hadi da mutane 9 da suka mutu.
“Marasa lafiyar ana kula da su a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Owo ya yin da ake gwajin tabbacin kamuwa da cutar a asibitin kwararru na Irua dake jihar Edo.
Gwamnan ya ƙara da cewa yanzu haka gwamnati ta fara bikin gangamin wayar da kan jama’a kan yadda za a kaucewa kamuwa da cutar.