Mazauna gidan yari a Nijeriya na bayyana farin cikin su da yadda kotuna ke daure manyan sanatoci da tsofaffin gwamnoni, wadanda ake zargi da wasu ayyukan rashin gaskiya da suka shafi almundahanar kudade.
Idan za a iya tunawa dai a sakamakon zarge zargen cin amanar dukiyar kasa da hukumar EFCC take zargin wasu tsofaffin gwamnoni da yi, wasu kotuna a garin Jos da Kaduna sun daure tsofaffin gwamnonin jihohin Filato da Kaduna, Jonah Jang da Ramalan Yero.
A dan zaman da ya yi a babban gidan yarin Jos, Sanata Jonah Jang mai wakiltar shiyyar Filato ta Tsakiya, kafin daga bisani kotu ta bayar da belinsa kan naira miliyan 100. Tsohon gwamnan ya biya kudin wutar lantarki da ake bin gidan yarin, wanda ya kasance tsawon lokaci babu wuta.
Shi ma tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero da hukumar EFCC ke zargin sa shi da wasu mutane da yin rub da ciki a kan kudaden yakin zaben shugaban kasa a shekarar 2015. Albarkacin watan Ramadan mai alfarma ya biya wa wasu fursunoni 31 kudaden tara da ake bukatar su biya kafin su samu ‘yanci.
Fursunonin da suka hada maza da mata, Musulmi ne da wadanda ba Musulmi ba, wadanda suke zaman wa’adi na wasu lokuta, bisa laifukan da suka aikata.