An Samu Karuwar Masu Dauke Da Cutar A jihar Borno- Hepatitis E


Hukumar kula da hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce ta sami karuwar yawan mutanen da ke dauke da cutar Hepatitis E a jihar Borno.

Hukumar NCDC ta gano hakan ne bayan ta gudanar da gwajin cutar kan mutane a kananan hukumomi 10 wanda ta fara yi daga ranar 17 zuwa 23 ga watan Yuli.

Hukumar ta ce gwajin ya nuna cewa mutane 562 daga kananan hukumomi Mobbar, Munguno, Chibok, Askira Uba, Bayo, Dikwa, Gubio, Mafa da Maiduguri na dauke da cutar.

Ma’aikatan ta ce an fara gano cutar ne a karamar hukumar Damasak wanda ke kusa da bodar Jamhuriyyan Nijar ranar 3 ga watan Mayu sannan aka sake gano cutar a karamar hukumar Ngala wanda ke kusa da kasar Kamaru.

A ranar 2 ga watan Yuli mutane 2,146 daga kananan hukumomi Ngala, Mobbar da Monguno sun kamu da cutar wanda har yanzu ana fama da shi a yankunan.

Hukumar NCDC ta rahoto cewa bayan gwajin da ta gudanar kan mutane ta gano cewa mata masu juna biyu da suka kai 52 sun kamu da cutar daga kananan hukumomin Ngala, Damask da Munguno sannan hudu daga cikin su sun mutu.

Hukumar NCDC ta bayyana cewa rashin samun tsaftatacen muhalli da ruwan sha na cikin abubuwan dake kawo cutar sannan jihar Borno ta fi fama da rashi tsaftatacen ruwan.

Daga karshe hukumar ta shawarci mutanen jihar da su tabbatar sun tsaftace muhallin su, abincin da za su ci da kuma ruwan da za su sha sannan a rage yawan yin cunkoso a daki daya domin guje wa kamuwa da cutar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like