An Samu Nasarar Tarwatsa Ƴan Ƙunar Baƙin Waken Dake Ƙoƙarin Kai Hari Jami’ar Maiduguri


Rundunar Sojan sama na musamman sun samu nasarar tarwatsa wasu ‘yan kunar bakin wake da suka yi kokarin kai hari a wurin kwanar daliban jami’ar Maiduguri a jiya Lahadi.

Kakakin Rundunar, Olatokunbo Adesanya ya ce, an gano ‘yan kunar bakin waken ne a lokacin da suka kusa kaiwa ga wuraren kwanar daliban inda daya daga cikinsu ya tarwatsa kansa yayin da sauran suka arce. Ya ce, a halin yanzu ana ci gaba da farautar sauran ‘yan kunar bakin waken bayan an samu kashe wasu daga cikinsu.

You may also like