An samu rahoton wata cuta a jihar Nassarawa da ake zargin farankamar biri ce 


Kwamishinan lafiya na jihar Nassarawa ya ce mutum daya aka samu da cutar da ake zargin farankamar biri ce a jihar.

Kwamishinan ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Lafiya babban birnin jihar.

Ya ce  tuni aka ɗauki jinin wanda ake zargi yana dauke da cutar inda aka tura dakin gwaje-gwajen  cututtuka da ke jihar Lagos inda ya kara da cewa gwamnati na jiran sakamakon binciken.

Ya ce gwamnatin jihar ta kara zage damtse wajen fadakar da mutane kan hanyoyin da ake kamuwa da cutar.

A cewar sa ma’aikatarsa ta hada kai da masu riƙe da masarautun gargajiya da kuma shuwagabannin addinai don su fadakar da mutane, musamman wadanda suke zaune a karkara domin sune suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Kwamishinan ya shawaraci jama’ar gari da su kai rahoton bullar duk wata bakuwar cuta da basu gamsu  da ita zuwa cibiyar lafiya mafi kusa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like