An Samu Tashin Bam A Kusa Da Ofishin Hukumar Kwastan Dake Maiduguri Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno suna bayyana cewa an kai harin kunar bakin wake a kusa da ofishin Kwastom dake ‘Custom Area’
Kakakin rundunar yan sandan jihar, Victor Isuku ya tabbatar da faruwar lamarin. 
Mista Isiaku ya ce an kai harin ne a yankin “Custom Area” dake cikin birnin jihar, sai dai ya ce binciken farko ya nuna cewa maharan ne kadai suka mutu. 
Harin wanda ya auku da misalin karfe goma na daren shejaranjiya, na zuwa ne a lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara 2017 a jiya Lahadi.

You may also like