An Samu Tashin Tagwayen Bama-Bamai A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Na Maiduguri. 


Kimanin mutane shida ne suka rasa ransu a yayin da wasu bama-bamai suna tashi a garin Maiduguri dake jihar Borno a safiyar yau Asabar, kamar yadda ganau ya bayyana. Bama-baman sun tashi ne a wurare daban-daban wanda ratan dake tsakanin su bai wuci kilomita guda ba.
Bam din farko ya tashi ne da misalin karfe bakwai a wani wurin shan shayi kusa dake sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi dake kusa da titin Maiduguri-Biu.
Bayan mintuna 35 kuma na biyun ya tashi a cikin babur mai kafa uku kusa da gidan mai na NNPC dake kan titin Damboa, inda wata da direban babur din suka rasu.
Wani jami’ain Banga, mai suna Alhaji Danbatta, ya bayyana cewa bam din farko ya tashi ne a yayin da wani dan kunar bakin wake ke shirin shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijirar na Bakassi.

You may also like