An samu wani dan kasuwa a jihar Kebbi da laifin shigo da sikari marar inganci 


Wani dan kasuwa mazaunin birnen Kebbi, Alhaji Moddibo Akilu, ya gurfana a gaban babbar Kotun Tarayya dake Birnin Kebbi kan zarginsa da ake na shigowa da buhun sukari 560 mara inganci daga ƙasar Barazil zuwa jihar ta kan iyakokin kasashen Jamhuriyar Nijar da Benin.

Mutumin da ake zargi an gurfanar da shi gaban mai sharia Simon Amebeda kan tuhume-tuhume guda Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya SON ce ta kama shi a ranar 28 ga watan Oktoba bayan da jami’anta suka kama wata mota makare da sukarin a babbar kasuwar birnin Kebbi.

Dan kasuwar ya ki yarda ya amsa dukkanin zargin da ake masa daga nan lauyansa ya nemi a bashi belinsa.

Kotun ta bada belinsa kan kuɗi ₦500,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.

An daga sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga  watan Disamba domin ci-gaba da sauraron shari’ar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like