An Sanar Da Kudin Kujerar Aikin Hajin BanaHukumar kula da aikin hajji ta Najeriya (NAHCON ) ta fara sanar da kudin aikin bana tare da umartar jihohi da su gaggauta  karbar kudaden kana su mika su ga hukumar.

Anyi wannan sanarwar a wurin wani   taron ganawa  da yake gudana   tsakanin hukumar lura da aikin hajji ta kasa da na jihohi da a ake gudanarwa a babban ofishin  hukumar dake Abuja. 

Ya zuwa yanzu dai jihohin Nassarawa, Neja, Kaduna, Kano, Adamawa, da Yobe sun sanar da kudin da mahajjatan da suka fito daga jihohinsu zasu biya. 

Yayin da alhazan da suka fito daga jihar Nassarawa zasu biya naira miliyan 1,544,894.16, ana sa ran na jihar Neja zasu biya miliyan 1,525,483.30, kaduna N1,535,503.68, Kano, N1,537,859.97, Adamawa, N1,530,101.08, sai kuma na jihar Yobe da za su biya N1,520,101.18 .
Wannan ya hada da kudin guzurin matafiya na dala $800.

Sai dai wani jami’in hukumar yace wannan kudi da maniyata zasu biya bai hada da kudin hadaya ba wanda maniyyatan zasu biya kan kudi N38,000.

Ana san ran hukumomin alhazan jihohin zasu mika kudaden ga bankin Jaiz wanda shine aka dorawa alhakin tattara kudaden. 

Ba Kamar yadda aka saba yi ba a baya na biyan kudi bai daya, a yanzu ko wacce jiha zata biya kudinta daban.

You may also like