
Asalin hoton, Real Madrid FC
An sanar da ranakun da Real Madrid za ta buga wasan mako na 31 da na 32 da kuma na 33 a gasar La Liga.
Real za ta buga wasan mako na 31 a La Liga da Girona ranar Talata 25 ga watan Afirilu a Montilivi.
Za kuma ta fafata a karawar mako na 32 da Almeria ranar Asabar 29 ga watan Afirilu a Santiago Bernabeu.
Real Sociedad za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 33 ranar Talata 2 ga watan Mayu a Reale Arena.
Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu, Real ta yi rashin nasara 3-2 a gida a hannun Villareal a karawar mako na 28 a La Liga.
Chelsea za ta ziyarci Real Madrid ranar Laraba 12 ga watan Afirilu, domin buga wasan farko a quarter finals a Champions League a Santiago Bernabeu.
Daga nan Real za ta ziyarci Cadiz a wasan mamo na 29 a La Liga ranar 15 ga watan Afirilu.
Wasan gaba da Real za ta yi shine ziyartar Chelsea a fafatawa ta biyu zagayen quarter finals a Champions League a Stamford Bridge ranar 18 ga watan Afirilu.
Real za ta yi fafatawar mako na 30 a La Liga ranar Asabar 22 ga watan Afirilu da karbar bakuncin Celta Vigo.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki 13 tsakaninta da Barcelona ta daya.
Ranar Litinin Barcelona ta tashi 0-0 da Girona a karawar mako na 28 a La Liga.